Wani jami’in dan sanda ya kashe kan sa, saboda an yi masa canjin wurin aiki zuwa Maiduguri.
Donatus Oyibe, an canja shi ne daga rundunar ‘yan sanda ta jihar Ebonyi, inda a can babban birnin jihar, Abakaliki ya kashe kan sa.
Oyibe dama dan asalin karamar hukumar Ebonyi ne ta jihar, rahotanni sun tabbatar da cewa ya tinjima cikin rijiya a daren Lahadi, bayan ya je da nufin debo ruwa.
Makwabtan sa dai sun ce tun daga ranar da ya karbi takardar canjin wurin aiki a ranar 28 Ga Agusta, 2017, sai duk fuskar sa ta canja, bai sake fara’a ba.
Majiyar ‘yan sanda ta ce ya na daga cikin rukunin ‘yan sandan Mobal da aka tura Maiduguri kwanan nan. ‘Yar sa mai suna Ukamaka, ta shaida cewa, mahaifin ta ya dauki bokiti ya ce zai debo ruwa a rijiya. Daga nan har bayan tsawon lokaci aka ji shiru.
“Bayan an bi sawu, sai aka tabbatar da cewa ya tunjuma cikin rijiya. Kuma aka tsamo gawar sa.
” Lokacin da mu ka isa bakin rijiyar, mun iske bokitin da ya tafi da shi, amma babu shi, kuma babu alamar sa. Daga baya an tsamo gawar sa a cikin rijiyar.”
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da mutuwar dan sandan.
Discussion about this post