Mabiya Kungiyar IPOB sun kona ofishin ‘Yan Sanda a jihar Abia

0

Mabiya kungiyar IPOB sun kona ofishin ‘yan sandan dake unguwan Ariaria, Jiahr Abia.

Kamar yadda kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar ya sanar ya ce matasan dauke da makamai ne suka kawo ma ofishin hari inda suka banka mata wuta.

” Bayan kona ofishin da suka yi sun lakada wa wani jami’in dan sanda dukan tsiya kafin suka kama gaban su.

Bayan haka kuma sun kai farmaki gidan kwamishina ‘yan sandan jihar inda suka farfasa wasu motoci a gidan.

Bayanai sun nuna sama da Hausawa 2000 ne suka gudu zuwa wasu sansanoni domin samun mafaka daga harin yan kungiyar IPOB din.

Sannan kuma an fatattaki wasu da suka kai hari unguwannin Hausawa dake garin Aba.

Share.

game da Author