Babu ruwan Fulani a harin da aka kai kauyen Ancha -Mohammed Nuru

0

Shugaban kungiyar makiyaya na jihar Filato Mohammed Nuru ya karyata zargin da rundunan ‘yan sanda ta yi cewa Fulani ne suka kai hari a kauyen Ancha wanda mutane 19 suka mutu.

Mohammed Nuru yace kwamishina ‘yan Sanda Peter Ogunyanwo bayan ya ziyarci kauyen Ancha din ne ya sanar da manema labarai cewa makiyaya ne suka kai harin.

‘‘Kwamishinan ‘yan sanda ya yi karya kuma karyan da ya yi ta isa ta rura wata sabuwar rikicin. A kan wani dalili ne zai ce Fulani ne suka kai wannan harin kuma an kama Fulani da suka aikata hakan?’’

Mohammed Nuru ya ce kamata ya yi a bincike kwamishinan ‘Yan Sandan don maganar da yayi zai iya tada wata rikicin.

Bayan haka shugaban kungiyan makiyayan ya ce kisan wani yaro bafilatani ne ya jawo wannan matsalar sannan mutanen da suka kashe yaron su uku sun gudu.

‘‘Ba gaskiya bane yadda ake ta korafin cewa kisan yaron ne ya tada rikicin. Mu na da kyakkyawar zamantakewa da mutanen kauyen Ancha kuma muna zargin wasu ne daga kauyen Dantanko suka aikata kisan.’’

‘‘Mun kai karan kisan yaron ga ‘yan sanda inda a ka kama mutanen biyar amma wandanda muke zargi ba a kama suba don sun gudu. To ta yaya Fulani kuma za su kai hari a wannan kauyen?’’

Ya ce sanadiyyar rikicin sun yi asarar dukiyoyin su da dama sannan suna zargin cewa wasu ‘yan uwansu biyu mutuwa suka yi domin sun bace kuma ba a gansu ba har yanzu.

‘‘Wasu mutanen sun harbe shanun Fulani guda tara a ranar Juma’a yayin da rikicin ta tashi’’.

Jami’an tsaro ranar Litini sun sanar cewa sun harbe mutane biyar wanda ake zargin da kisan da aka yi a kauyen sannan soja daya ya rasa ransa.

Share.

game da Author