Gwamnatin jihar Kaduna ta kara jaddadawa mutanen jihar cewa dokar hana yin znga-zanga da tattaki ko wani iri na nan daram dam a jihar Kaduna.
Mai taimaka wa gwaman jihar Kaduna kan harkokin yada labarai Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan bayan zaman da kwamitin tsaron jihar tayi yau a jihar.
Ya ce gwamnatin ta yi haka ne saboda ta samar wa mutanen jihar da tsaro da kariya ga dukiyoyinsu.
Ya ce gwamnatin a jihar za ta hukunta duk wanda ya karya doka a ko shi waye.
Bayan haka gwamnan jihar Nasir El-Rufa’I ya mika godiyarsa ga jami’an tsaron jihar, sarakunan gargajiyya,shugabanin addini, kungiyoyi masu zaman kansu kan gudunmuwar da suke ba jihar don ganin an zauna lafiya da juna a ko-ina- a fadin jihar.
Bayan haka gwamnati ta sa naira 100,000 ga duk wanda ya bata sanarwan inda wani Yakubu Amos yake.
Ta ce Amos ya gudu ne tun bayan samun shi da akayi da hannu dumu-dumu a rikicin karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya ce duk wanda ya basu bayanai akan inda za a ganshi zai samu ladan naira 100,000.