1 GA WATAN MUHARRAM: Aregbesola ya bada hutu a jihar Osun

0

Gwamnatocin jihohin Osun da Kano sun sanar da bada hutun a jihohinsu gobe a jihar Osun sannan Kano ranar Juma’a domin murnan shiga sabuwar shekaran musulunci na 1439.

Gwamnan Jihar Osun Aregbesola ya ce tun a shekarar 2012 jihar ta amince da dokar yin hutu duk ranar 1 ga watan Muharram.

Gobe Alhamis ne daya ga watan Muharram.

A jihar Kano za a yi hutun ne ranar juma’a domin shiga sabuwar shekarar musulunci.

Share.

game da Author