Fayose ya kalubanci Lai Mohammed ya bayyana sunayen masu daukar nauyin Biafra

0

Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya kalubalanci Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed da ya fito ya bayyana wadanda ya ce su ke daukar nauyin kungiyar fafutikar kafa Biafra daga kudaden da suka wawura a gwamnatin Najeriya.

Lai dai ya yi wannan ikirari ne ranar Lahadi a Lagos a wurin wani taro, inda ya ce aniyar masu daukar nauyin ‘yan Biafra shi ne su karkatar ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari daga kyakkyawan ci gaban da ta aiwatar da kuma wanda gwamnati ke aiwatarwa.

Bayanan da Lai Mohammed ya yi sun biyo bayan wani furucin da jam’iyyar APC ta yi cewa Gwamnan na Ekiti, Ayo Fayose ne ke daukar nauyin su tsagerun da ke neman kafa Biafra.

A ta bakin kakakin yada Labarai na Fayose, Lere Olayinka, gwamnan ya ce, lokaci fa ya yi da za a fara titsiye Lai Mohammed domin ya kawo hujjojin zarge-zargen da ya ke yi masu kama da sharri, kage da kazafi.

“Sama da watanni 20 da suka gabata fa Lai Mohammed ya ce ‘yan Najeriya 55 sun sace sama da naira tiriliyan 1.34, tsakanin 2013 zuwa 2016. Amma har yau ya yi mirsisi ya ki kawo sunayen su.”

Daga nan sai Fayose ya kara da cewa idan Lai ya manta, to shi bai manta ba cewa, ranar 10 Ga Yuni, 2013, Lai ya ce bai kamata a haramta kungiyar Boko Haram ba, kuma bai kamata a sake wa Najeriya sabon tsarin mulki da fasali.

Share.

game da Author