Gwamnatocin Sokoto da Zamfara sun kammala gyara titin Sokoto zuwa Gusau

1

Gwamnatocin Sokoto da Zamfara sun kammala gyaran titin Gwamnatin Tarayya, wada ya tashi daga Sokoto zuwa Gusau.

Kakakin gwamnan jihar Sokoto, Imam Imam ne ya fitar da wannan bayani yau Litinin cikin wata takarda da ya raba wa manema labarai a Sokoto.

Titin dai shi ne ya hada Sokoto, Zamfara, Kebbi da Jihar Katsina, har ya dangana da cikin jihar Kaduna.

Ya ce duk an gyara shi a kan kudi naira miliyan 100.

“Jihohin guda biyu ne su ka hadu don gyaran titin, wanda shi kadai ne ya hada yankin da Jamhuriyar Nijar.

“Ya na daya daga cikin tituna masu muhimmanci a yankin Arewa maso Yamma.

Dama kuma abin da ake bukata, shi ne ya kasance babu sauran rami ko da kwaya daya a kan titin. Hakan kuwa ta tabbata.

Ya kuma ce yayin da jihar Zamfara ce ta bayar da kudin gyaran hanyar daga Gusau zuwa Tureta, ita kuma jihar Sokoto ta bada kudin gyaran hanyar daga Tureta zuwa Sokoto.

Imam yace za su rubutawa gwamnatin tarayya kudaden da su ka kashe domin a biya su, tunda hakkin gwamnatin tarayya ne ta gyara titin.

Gyara titin kuma inji shi, zai kara habbaka zirga-zirga, musamman safarar amfanin gonar da ake yawan samu a yankin. Kana kuma zai rage da saukake yawan hadurra.

Share.

game da Author