Jami’ar Ilorin ta fara jarabawar tantance daliban da ta dauka a shekarar karatu ta 2017. An fara yi wa wadanda su ka cika Fom din neman shiga jamm’ar su 64,000 wannan jarabawa ce a yau Litinin.
Kunle Akogun, Mataimakin Darakta, shi ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai wannan bayani cewa daliabai 104,000 ne su ka cike fom din neman shiga jami’ar, inda za a dauki 11,000 kacal daga cikin su.
Ya kuma shaida wa NAN cewa maki 180 ake bukata daga duk dalibin da za a dauka a jami’ar, a matsayin mafi karancin makin da dalibi zai kasance ya samu.
Ya na mai alfahari da cewa, jami’ar Ilorin ta yi suna wajen bayar da ilmi a cikin tsari da kayyadajjen jadawali, dalili kenan ta kasance wadda aka fi rububi shiga a Najeriya.
A cewar sa, wannan mulki na shugaban jami’ar mai ci yanzu, zai ci gaba da kasancewa ya kara daga martabar ilmi a jami’ar.