Yau Litini 11 ga watan Satumba kungiyar kwadigo NLC reshen jihar Zamfara ta sanar da shiga yajin aiki na bai daya a fadin jihar.
Shugaban kungiyar Bashir Marafa ya sanar da hakan a hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya ta yi da shi ranar Lahadi a Gusau.
Ya ce sun shiga yajin aiki ne bayan gazawa da gwamnatin jihar tayi na cika alkawurran da ta dauka wa ma’aikatan jihar bayan wa’adin kwanaki 21 da suka bata ya cika.
Dalilan da ya sa ma’aikatan suka shiga yajin aikin sun hada da :
1. Rashin maida hankali wajen cika alkawuran da gwamnati ta dauka wa ma’aikatan jihar tun shekaru shida da suka wuce.
2. Wasu ma’aikata har yanzu suna karbar kasa da Naira 18,000 a matsayin karancin albashi.
3. Gwamnatin jihar ta ki kara wa ‘yan fansho kudin fansho wanda ya kamata a yi shekaru biyar da suka wuce.
4. Rashin daukan ma’aikata musamman yadda wasu suka yi ritaya ko kuma canza wurin aiki .
5. Rashin biyan albashin ma’aikata 1,400 da ta dauka tun a 2014.
6. Gwamnati ta yi watsi da kungiyar kwadugo musamman game da kudin da ta karba daga gwamnatin tarayya na (Bailout Funds)
Bayan haka a kwanakin da suka gabata kungiyar ta gana da sakataren gwamantin jihar Abdullahi shinkafi ko za a iya hana yajin aikin.
A yanayin da ake ciki mai ba gwamnan shawara akan harkokin yada labarai Ibrahim Dorasa ya fada wa manema labarai cewa an soke wannan wa’adin kawanaki 21 da kungiyar ta bada.
Ya ce gwamnan jihar Abdul’aziz Yari ya umurci shugabanin kungiyar NLC din da su kawo ainihin sunayen ma’aikatan da gwamnatin ta ki biya.