Sanata Kanti Bello ya rasu

0

Da safiyar yau Talata ne aka bada sanarwar rasuwar Sanata Kanti Bello. Ya rasu ne yau a Abuja.

Wata sanarwar da ta fito daga Kabir Faskari, ta ce “an umarce ni da na shaida muku cewa Allah ya karbi ran Sanata Kanti Bello yau Talata da sassafe, a Abuja.

Ya ci gaba da cewa, ” za a bada sanarwar lokacin da za a yi wa gawar rasa Sallah nan ba da dadewa ba.”

Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Ingawa, Sabi’u Ingawa ya tabbatar da rasuwar Kanti.

Sanata Kanti Bello shi ne Sanatan Shiyyar Daura, daga Jihar Katsina, tsakanin 2003-2007 da kuma 2007-2011.

Shi ne kuma Shugaban Kamfanin da ake sarrafa karfafa, KSRMC, Katsina.

PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa Kanti ya yi fama da rashin lafiya a tsaitsaye kafin rasuwar sa.

Share.

game da Author