A yau Talata Kungiyar Malaman Jami’o’I ta Kasa za ta sake zama teburin shawara da Gwamnatin Tarayya, domin cimma yarjejeniyar yadda za a warware matsalar yajin aiki da malaman ke yi.
Premium Times Hausa ta samu tabbatacin zaman wanda mataimakin daraktan yada labarai na Ma’aikatar Kwadajo da Samar da Ayyuka, Samuel Olowookere ya sanar.
Ya ce wakilan gwamnatin tarayya za su hada da Ministocin Ilimi da na kudi, Hukumar Kudaden Shigar Albashi, da kuma Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa ta Kasa, NUC.
Haka nan kuma ana sa ran Shugaban Kungiyar Kwadago na Kasa zai halarci taron tattaunawar.
Shugaban Kungiyar Malaman Jami’0’I ta Kasa, ASUU, Biodun Ogunyemi ne ake sa ran zai jagoranci tawagar wakilan malaman jami’o’i.
Ana kyautata zaton cewa gwamnatin Nijeriya ta ce ta nuna kyakkyawan kudirin aniyar amgance wannan matsala da ta dakile fannin ilmi.
A wata sabuwa kuma, Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya, NASU da ta Kungiyar Malaman Fasaha ta kasa, za su kada kuri’ar raba gardama a narar Litinin domin neman rinjayen ra’ayin tafiya yajinn aikin da sai-Baba-ta gani.
Kungiyar ta ce ta na cike da mamaki tare da bacin rai, ganinn yadda gwamnatin tarayya ke zaman tattaunawa da kungiyar malaman jami’o’i kadai, ba tare da zama da ta su kungiyar ta ma’aikatan jami’o’i ba, duk kuwa da cewa gwamantin na sane da dimbin matsalolin da su ka yi musu kaka-gida shekara da shekaru.
Ana sa ran za su yi na su taron raba-gardamar a hedikwatar su da ke Abuja.
Discussion about this post