Gobara: Wuta ta lashe dakunan daliban jami’ar Filato

0

Jami’ar fasaha dake jihar Filato ta fada cikin halin rudani yayin da sashen dakunan kwanan dalibai matan makarantar ta kama da wuta da safe da misalin karfe 8:30 zuwa 11:44 na ranar Litini.

Wasu daliban sun gudu lokacin da gobarar ta fara inda wasu sun nuna jarunta ta hanyar kokarin kashe wutan amman duk da haka ba a samu nasaran haka.

Yusuf Ade da ke aikin gadi a makarantan ya ce daliban sun tafi aji a lokacin da gobarar ta fara amma ko tsinke ba a ciro ba daga dakunan daliban.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta ce hukumar kashe gobara ta jihar ta iso wajen wutan ne bayan gobarar ta cinye komai dake dakunan.

Wani jami’in makaranta Dauda Gyemang ya ce “godiya ga Allah babu ran da muka rasa.”

Yayi bayanin cewa iskar da ake amfani da shi wajen girki ‘Cooking Gas’ da turanci ne ta fashe wanda hakan ya tada da gobarar.

Ya ce duk da cewa hukumar makarantan ta kafa dokar hana yin girki a dakunan kwanan daliban domin guje wa irin hakan amma taurin kan wasu daliban ya suka karya dokar.

Dauda Gyemang ya yi kira da daliban musamman mata da su kwantar da hankalinsu domin makarantan zata samar musu da wurin da za su ci gaba da kwana.

Ya ce ba da dadewa ba makarantan za ta gyara dakunan da gobarar ta kama.            

Share.

game da Author