Boko Haram sun kashe masunta 31 a Tafkin Chadi

0

Gwamnan Jihar Barno, Kashim Shettima ya tabbatar da cewa Boko Haram sun kashe masunta 31 a Baga, cikin Karamar Hukumar Kukawa, a Jihar Barno.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ya ruwaito cewa gwamnan ya bayyana haka, a ranar Talata a yayin rabon abincin agaji wanda Kungiyar ECOWAS ta kasashen Afrika ta Yamma ta taimaka wa ‘yan gudun hijira a sansanonin su, a Maiduguri.

Ya ce harin na tabbatar da cewa har yanzu dai Boko Haram na nan su na kaddamar da munanan hara-hare, su na karkashe mutane a yankin Tafkin Chadi.

Shettima ya ce har yanzu jami’an sojoji da sauran jami’an tsaro ba su kai ga tantance rahoton ba.

” Wani ya kira ni da safiyar nan, ya shaida min cewa Boko Haram sun kashe masunta 31 a Tafkin Chadi.

” Su kuma jami’an tsaro ba su kai ga tabbatar da rahoton ba, don haka mu na jiran su tabbatar da hakan.

” Hakan na nuni da irin mummunan rikicin da mu ke fuskanta a Barno, inda masu karyar Jihadi ke ci gaba kashe mutane a Tafkin Chadi.

Shettima ya jinjina wa irin kokarin da jami’an tsaron sojoji ke yi wajen kokarin kawo karshen ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

Kamfanin Dillancin Labarai dai ya ruwaito cewa an kashe masunta 31 a Tafkin Chadi, a ranakun 5 da 6 Ga Agusta, 2017.

Wata lambar waya, mallakar wani dan CJTF, ya kira da boyayyen suna cewa an kashe masunta 14 a Duguri, 17 kuma a Dabar-Wanzam.

Share.

game da Author