Illoli 5: Shin ko ka san kwanciya a katifa mara kyau na sa yawan Mantuwa?

0

Wani likita a babbar asibitin dake Abuja, Ikechukwu Amadi ya gargadi mutane kan guje wa kwanciya a katifar da bai kamata ba wato mara kyau saboda illolin da yake sa wa jikin mutum.

Ya ce babbar illar da kwanciya a katifar da bai kamata ba ke kawo ya hada da rashin samun isashiyyar barci wanda rashin shi ya kan jefa mutum cikin wani mawuyacin hali kamar su damuwa,tabuwar hankali da sauran su.

Illolin hakan ya hada da:

1. Kwanciya a katifar da bai kamata ba na kawo ciwon baya.

2. Yana hana mutum samun isashshen barci wanda rashin hakan ke sa wasu yawan fushi.

3. Yan kawo yawan yin minshari.

4. Kwanciya a katifar da bai kamata ba na rage karfin garkuwan jiki wanda hakan na iya sa mutum kamuwa da cututtuka kamar su mura, ciwon kai da sauran su.

5. Yana sa yawan mantuwa.

Share.

game da Author