Babu laifin da Buhari yayi rashin dawowa da baiyi ba har yanzu – Majalisar Dattawa Majalisar

0

Majalisar Dattawa ta sanar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai aikata laifi ba rashin dawowa da bai yi ba har yanzu daga kasar Britaniyya.

Yau Kwanan Buhari 93 a kasar Britaniya in da ya ke ganawa da likitocinsa.

Wasu tsirarun mutane suna gudanar da zanga-zangar kira ga shugaban kasa ya sauka daga kujerar mulkin Najeriya a Abuja.

Dalilin haka ne ya sa majalisar dattawa ta fitar da sanarwan cewa Buhari bai aikata laifin komai ba domin duk abin da dokar kasa ta umurta ya yi ya aikata.

“ Doka ta ce idan shugaban kasa zai yi tafiya ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa wanda Buhari ya yi hakan.

Saboda haka ban ga inda yayi laifi ba da har wasu zasu fito suna cewa dole sai ya dawo ko ya sauka daga kujerar shugabancin Najeriya.

“ Saboda haka muna kira ga wannan kungiya da ke yin zanga-zanga da su mai da wukan. Su ci gaba da yi wa shugaban kasa addua da mataimakinsa da yake jan ragamar mulkin kasar yanzu.”

“ Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo na yin abinda ake bukata a kasar kuma hakan doka ce ta bashi wannan iko.” Inji Aliyu Abdullahi, Kakakin Majalisar Dattawa.

Share.

game da Author