Duk da dokar hana bara da gwamnatin jihar Kano ta yi a kwanakin baya, yanzu dai mabarata sun dawo bara a titunan Kano gadan gadan.
Wani mai bara da ya tattauna da wakilin mu a Kano ya ce dawo wa sana’ar bara ya zama dole domin wahala ya ishe su.
“ Kullum nake shigowa garin Kano daga kauyen da nake don yin bara saboda talauci yayi mini katutu.
Wata mabaraciya mai suna Batula ta ce duk da hanin idan ta matsu takan fito tayi baran na dan wani lokaci.
Darektan hukumar Hisba, Abba Sufi ya ce sun kama mabarata da yawa saboda gwamnati ta basu sana’a da jari domin sana’ar tasu tun a lokacin da a ka hana bara a Kano, saboda haka bas u da dalilin dawowa titunan garin.
Discussion about this post