ZABEN 2019: Ganduje ya ci taliyar karshe, cewar Kwankwaso

1

Wani na hannun damar Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya maida wa Sanata Bola Tinubu martanin cewa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ba zai ci zabe ba a 2019.

Kwamishinan Hakokin Cikin Gida na gwamnatin Kwankwaso, Aminu Gwarzo, shi ne ya yi wannan martanin dangane da yabon da Tinubu ya yi Ganduje cewa ya ma ci zaben 2019 ya gama.

Kwankwaso dai a yanzu shi ne Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya.

A ranar Talata ne Gwarzo ya bayyana cewa ai tun cikin shekarar da ta gabata ne Kanawa su ka yanke shawarar ba za su sake zaben Ganduje ba a 2019.

“Mu ba mu so mu tsaya mu n aka-ce-na-ce da Sanata Tinubu, amma dai ni abin da na ke so na ce shi ne, Asiwaju fa daga filin jirgi da aka dauke shi, ba a zarce ko’ina da shi ba sai cikin gidan gwamnati, amma bai san abin da ke faruwa kuma bai san halin da al’ummar karkara ke ciki ba. Bai kuma san halin da sauran ‘yan jihar suke gaba daya su ke ciki ba, amma ya yi azarbabin yanke hukuncin cewa wai a 2019 Ganduje ya ci zabe ya gama.”

“Mun san Asiwaju mutum ne mai gaskiya, amma da ya san halin da ake ciki a Kano, da bai yi subul-da-bakan bai wa Ganduje kujerar gwamnan Kano a zaben 2019 ba.

Gwarzo ya kara da cewa ai tuni Ganduje ya raba hanya da Kanawa, don haka su ma su ka ce shi kadai za su bari a kan hanyar da ya ke kai a yanzu, idan zaben 2019 ya zo.

A karshe ya ce da Tinubu ya kai ziyara a wasu wurare ko kasuwannin cikin Kano, to da ya ga kuma ya ji yadda aka gaji da Ganduje.

Share.

game da Author