Kungiyar Amnesty ta zargi sojojin Kamaru da gana wa mayakan Boko Haram azaba

0

Daruruwan ‘yan Boko Haram da ke tsare a hannun dakarun sojin kasar Kamaru na dandana kudarsau daga sojojin dake tsare da su a kasar.

Kungiyar Amnesty International ne ta fitar da wannan bayanai.

Ta ce ta sami sahihancin haka ne bayan amfani da na’urorin hangen nesa ta sama da ta kasa a sansanonin da ake ajiye da ‘yan Boko Harm din a kasar Kamaru.

Shaidun kungiyar Amnesty International sun nuna yiwuwar cewa wadannan sansanonin sojan Kamaru da sauran wuraren tsare mutane har yanzu ana tsare mutane da dama wadanda ake gana masu gwalegwale da mummunar azaba.

Ga cikakken bayanin kamar yadda Amnesty ta fitar:

Kamaru: Rahoton kungiyar kare hakin jama’a ta Amnesty ya bayyana yadda aka yi amfani da matsanancin ganawa mutane azaba a yaki da aiyyukan ta’adanci na kungiyar Boko Haram.

An ganawa wadanda aka tsare azaba da lakada masu duka ga shiga cikin mawuyacin hali da azabtar da su ta hanyar nutsar da su a ruwa, yayinda wasunsu aka gana masu azaba har suka kai ga mutuwa.

An samu yawaitar azabtar da jama’a a wurare guda 20 da suka hada da sansanonin soja guda biyu da wasu sansanonin biyu da jami’an leken asiri ke kula da su da gidan wani da kuma wata makaranta.

Kungiyar ta yi kira ga Amurka da sauran kawaye na kasa da kasa da su binciki jami’an sojojinsu domin yiwuwar suna da masaniya a kan azabtar da jama’a da aka yi.

Daruruwan mutane a kasar Kamaru da ake zarginsu da goyon bayan kungiyar Boko Haram a mafi yawan lokuta ba tare da wata shaida ba, jami’an tsaro na gana masu azaba, inji kungiyar Amnesty International a wani sabon rahoton da ta wallafa a yau.

Ta hanyar amfani da mutane masu yawa da suka bada shaida hadi da shaidu da aka samu na hotunan da tauraron dan adam ya samar, da wasu hotuna da ma shaidu na bidiyo, rahoton mai taken “Dandalin azabtar da jama’a na kasar Kamaru: take hakokin bani adama da miyagun laifuffukan yaki ,a yaki da kungiyar Boko Haram’’ an tattara irin wadannan cin zarafi har guda 101 na mutanen da aka tsare ba tare da barin a gansu ba, inda aka rinka gana masu mumunar azaba a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2017 a wurare daban –daban fiye da guda 20.

“Mun yi ta nanatawa karara da babbar murya muna yin Allah wadai da miyagun laifuffukan yaki da kungiyar Boko Haram ta aikata a kasar Kamaru. Amma duk da haka babu dalilin da zai halatta aikata wannan mumunan aiki da jami’an tsaron Kamaru suke yi na yawaitar ganawa al’ummar kasar Kamaru mumunar azaba, mutanen da a mafi yawan lokuta akan kama su a tsare su ba tare da wata sheida ba, a sanya su fuskanci azabar da ta wuce kima,’’ Inji Alioune Tine, Daraktan kungiyar Amnesty International mai kula da shiyyar Afrika ta yamma da ta tsakiya.

“Wannan mumunan karya dokoki ya kai mizanin aikata miyagun laifufukan yaki. Bisa la’akari na karfin shaidun da muka bankado, dole ne ga hukumomin Kamaru su fara bincike mai zaman kansa a kan mutanen da ake tsare da su a gidajen yari da ake azabtar da su, tare da hanasu ganawa da kowa, wanda ya hada da mutanen da nauyi ke kansu’’

A watan Afrilun shekarar nan ta 2017 kungiyar Amnesty International ta rubutawa mahukuntan kasar Kamaru wasika domin ba su kwafin abubuwan da ta gano a wannan rahoto, to sai dai babu wani martani da gwamnatin ta bayar, kuma ta ki yarda da dukkanin bukatu na neman ganawa a kan batun.

Kungiyar Amnesty International ta yi kiyasin cewa tun daga shekarar 2014 kungiyar Boko Haram ta kashe fiye da fararen hula 1,500 a Kamaru, tare da sace wasu da dama.

“Yanke shawara a kan rayuwa ko mutuwar duk wanda ake tsare da shi”

Mutanen da aka ganawa azaba sun bayyana kimanin nau’oin azabtarwa guda 24 da aka gana masu. A daya daga cikin irin wadannan da suka bayyana da suna ‘’Akuya’’ ana daure hannuwansu a bayansu kafin a lakada masu duka. A wani nau’in azaban kuma da suka bayyana da ‘’Lilo’’ ana sagale mutanen ta hanyar sanya hanuwansu a baya suna lilo kafin a yi ta dukansu.

Mafi yawan mutanen an gana masu azaba ne a wurare biyu: hedikwatar kai daukin gaggawa ta BIR da ke Salak kusa da arewacin garin Maroua, da kuma wani wurin da ke kusa da hedikwatar a babban birnin Yaounde wanda ke karkashin kulawar sashin kula da bincike na hukumar liken asiri ta Kamaru da ke kusa da majalisar dokokin kasar.

Ta hanyar amfani da tsarin bada bayanai da sifanta abubuwa daga mutanen da aka taba tsare su, faifan bidiyo da hotunan da aka dauka ta hanyar amfani da tauraron dan Adam, tawagar kwararru a fanin zane-zanen da binciken masu aikata laifuffuka sun samar da yadda aka mayar da sashin da ke a Salak da makaranta a Fotokol suka koma sansanin soja.

A Salak dai akwai wuraren tsare jama’a guda biyu wadanda suka kai kimanin tsawon mita 9 fadinsa kuma ya kai mita

5. Kowanne daga cikinsu na da mutanen da suka kai 70 a ciki. A kan azabtar da mutanen da ake tsare da su a wannan wuri ne a wani daki da ake tuhumarsu wanda ake kira da ‘’dakin DGRE’’ wanda yake kusa da ofishin wani babban jami’i. Mutanen da aka taba tsare su sun bayyana wannan jami’i a matsayin wanda yake bada umurnin a gudanar da tuhuma, kamar yadda daya daga cikin mutanen yace jami’in ne ke da ikon yanke shawara a kan rayuwa ko mutuwar duk wanda ake tsare da shi.”

Samou (wannan ba sunansa na gaskiya ba ne), wanda aka kame shi a watan Maris na shekarar 2016 ya shaidawa Amnesty International yadda aka yi mashi tambayoyi na tuhumarsa a Salak kwanaki kalilan bayan da aka kama shi:

“Sun tambayeni in fada masu idan nasan ‘yan kungiyar Boko Haram. Wannan a lokacin da suka daure hannuwana da kafafuwana a bayana Kenan, sannan suka fara dukana da wayar lantarki, sannan suna watsa man ruwa. Sun yi man dukan da na kusa mutuwa’’.

Mohamed (ba sunansa na gaskiya ba ne) ya kwashe watanni shida yana tsare a inda babu ikon wani ya ganshi kuma an yi mashi tambayoyi tare da azabtar da shi a lokutta daban-daban a Salak. Ya shaidawa Amnesty International cewa:

“Sojojin sun ce mana mu bada shaida, suka ce idan bamu bada shaida ba zasu kawo mu Yaounde su kashe mu. Mun basu amsar cewa mun zabi a kashe mu yafi mana mu bada shaida a kan abinda bamu san komai a kansa ba. Haka suka yi ta dukanmu na tsawon kwanaki hudu’’.

Kasancewar sojojin Faransa da na Amurka a Salak

Haka nan rahoton ya yi bayanin kasancewar sojojin Amurka da na Faransa a sansanin BIR da ke Salak, tare da kira ga gwamnatocin wadannan kasashe da su gudanar da bincike a kan irin hannun da sojojinsu ke da shi wadanda aka ajiye su a Salak, ko kuma suke yawan kai ziyara a wurin, ko ma dai suna da masaniya a kan wannan haramtaccen wurin da ake rufe mutane ake azabtar da su .

Wakilan kungiyar Amnesty International kai tsaye sun lura cewa a daya daga cikin ziyarar da sojojin kasar Farnsa ke kaiwa a wurin, akwai mutane da dama da aka tsare su a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2016, cewa sun gani kuma ma sun ji turawa na magana da harshen Turanci a sansanin kuma ma wasunsu na cikin kayan soja. An tabbatar da wannan ta hanyar shaidar hotunan da aka dauka da bidiyo wanda ya nuna sojojin Amurka, wasunsu wadanda aka girke su a sansanin ne.

“Bisa la’akari da yiwuwar tsawon lokacin da sojojinsu suka yi a wurin, akwai bukatar Amurka da sauran kasashen da ke kawance su gudanar da bincike don gano irin abinda sojojin nasu suka sani a kan wannan haramtaccen wurin tsare jama’a, tare da gano ko suna sane da zabtar da jama’a da aka yi a sansanin na Salak, ko sun dauki wa ni mataki na kai rahoto ga manyan jami’ansu, ko kuma mahukuntan kasar Kamaru,’’ inji Alioune Tine.

Tun a ranar 23 ga watan Yuni na 2017 kungiyar Amnesty International ta rubutawa ofishin jakadancin kasashen Amurka da na Faransa da ke Kamaru tana bukatar karin bayani a kan abinda jami’an sojojinsu suka sani da abinda suka bada rahoto a kai. Ofishin jakadancin Amurka ya bada amsar wasikar a ranar 11 da watan Yuli kuma za’a iya samun amsar wasikar tasu in aka latsa nan. Babu amsar da aka samu daga ofishin jakadancin kasar Faransa.

An yi amfani da makaranta a matsayin sansanin azabtar da jama’a

Kungiyar Amnesty International ta gano wata makaramta da ke a arewacin garin Fotokol wace BIR suka yi amfani da ita a matsayin sansanin soja tun a watan Mayun shekarar 2014. Masu bincike sun yi tambayoyi ga mutane shida da aka taba tsare su tare da azabtar da su a sansanin a tsakanin watan Disambar shekarar 2015 zuwa watan Maris na shekara 2016, sun yi nazarin faifan bidiyo da ya nuna sojojin BIR da ke sanye da kayan soja suna ganawa fursonin da aka tsare azaba. A wani sashi na bidiyon an ga sojoji da yawa suna jan wani mutum a kasa na kimanin tsawon mita 50, suna dukan wasu da aka rufe masu fuskansu da sanda ta ice mai kaifin gaske.

A karshen shekarar 2016 ne aka bude makarantar don ci gaba da karatu, amma har zuwa watan Yunin 2017 jami’an tsaro na BIR suna amfani da wani sashi na makarantar, kimanin mutane tara ake tsare da su a wurin. Amfani da makarantar a matsayin sansanin soja a dai dai lokacin da yara ke amfani da shi ya sabawa kudrin da ke kan kasar Kamaru a karkashin dokar kasa da kasa ta kare fararen hula da ke a hali na rigingimu da makami, domin ta haka an jefa yaran cikin hatsari.

An gane jami’an tsaro masu matsakaicin da manyan mukami

A yayin da ake ci gaba da azabtar da mutane wanda jami’an tsaro masu matsakaita da manyan mukami na BIR da na DGRE ke yi, mutanen da aka ganawa azaba sun gane manyan jami’an hukumar tsaron Kamaru ta DGRE da su suke shiga ana yi wa wadanda aka tsare tambayoyi na tatsar bayanai tare da su. Yawa da yawaitar karya dokokin da kuma wuraren da aka yi amfani da su ya nuna matukar yiwuwar manyan jami’an tsaro da suke a wurin a Salak zasu iya sanin abinda ke faruwa. Wannan ya nuna alamun cewa basu dauki wani mataki na hana afkuwar hakan ba, ko kuma hukunta wadanda suka karya doka.

A Salak an gano fiye da mutane 50 da aka azabtar da su a daki guda. Hotunan tauraron dan Adam ya nuna wannan dakin a wannan ginin da manyan jami’an BIR ke amfani da shi, inda aka tsare fiye da mutane 70 a lokaci guda, kuma a wurin ne aka azabtar da su, kuma wurin ne da yake da nisan mita 110 daga ofishin manyan jami’an BIR.

“ Dole ne a gudanar da bincike a kan manyan jami’in da ikon kula da wannan wuri ke a karkashin kulawarsu, domin tuhumar nauyin da ke kansu da ma zargin tsare mutane a wurin da ba wanda ya isa ya gansu, ga gana masu azaba da mutuwar wasu a wurin, tare da bacewar wasu’’. Inji Alioune Tine.

Shaidun kungiyar Amnesty International sun nuna yiwuwar cewa wadannan sansanonin sojan Kamaru da sauran wuraren tsare mutane har yanzu ana tsare mutane da dama wadanda ake gana masu gwalegwale da mummunar azaba.

Domin Karin bayani sai a tuntubi ofishin yada labaru na kungiyar Amnesty International da ke a Dakar, Senegal, +221 77 658 62 27 or +221 33 869 82 31; ko a aika da sakon Email; press@amnesty.org; ko sadibou.marong@amnesty.org Ko kuma ta Twitter: @AmnestyWaro.

Share.

game da Author