Yadda Boko Haram su ka kashe sojoji 9 da malaman Jami’ar Maiduguri 4

0

Garkuwar da Boko Haram su ka yi wa ma’aikatan gano danyen mai wadda ta haifar da kashe sojoji tara, ta kuma janyo rasa rayukan wasu mutane har 18 da su ka hada har da wasu ma’aikatan hako danyen man, kamar yadda PREMIUM TIMES ta tabbatar.

Wadanda tsautsayin ya ritsa da su, sun hada da masana ilmin kimiyya, injiniyoyi da kuma ma’aikatan tsaro na sa-kai da aka fi sani da Civilian JTF. An dai yi musu kwanton-bauna ne a kusa da kauyen Jibi da ke cikin Karamar Hukumar Gubio,yankin a lokacin da su ke kan hanyar aikin gano rijiyar mai a Yankin Tafkin Chadi.

Kamfanin mai na kasa, NNPC, wanda shi ne ke da alhakin aikin hakowa ko gano danyen man, ya bayyana cewa jami’an sa 10 na cikin tawagar, amma sauran ma’aikatan man, duk malamai ne daga fannin nazarin albarkatun kasa daga Jami’ar Maiduguri, wadanda aka dauka aikin gano danyen man fetur.

Bayan an yi garkuwa da su ne a ranar Talata, sojojin Najeriya kuma su ka kaddamar da yakin ceto rayukan su.
Kakakin rundunan askarawan kasar nan, Usman Sani, ya bayyana cewa an ceto rayukan dukkan ma’aikatan NNPC, amma kuma sai da aka yi asarar sojoji tara.

Yawan wadanda suka rasarayukansu

PREMIUM TIMES ta ji daga majiya mai tushe cewa yawan wadanda su ka mutu daga bangaren sojoji da malaman Jami’ar Maiduguri, ya shige adadin da Sani Usman ya bayyana. Majiyar ta kuma ce ba a ceto rayukan ko daya daga cikin su ba, an samo su a mace.

Shi dama Burgediya Janar Usman bai fadi adadin yawan wadanda aka ceto da rayukan su ba.

Akalla mutane 18 ne su ka rasa rayukan su daga harin da aka kai. Haka wani babban jami’in soja ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Daga cikin mutane 18 da aka harbe, 12 daga cikin su mambobi ne na jami’an tsaro na sa-kai, CJTF, sai kuma malaman Jami’ar Maiduri hudu da su ka hada har da masu PhD. Haka PREMIUM TIMES ta samu tabbaci.

PREMIUM TIMES ta ki bayyana sunayen wadanda aka yi asarar, har sai an kai ga sanar wa iyalan su tukunna.

Tuni dai aka kwaso gwarwakin su aka ajiye a dakin adana gawawwaki na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.

Jamai’an asibitin ba su yi magana ba, sai dai kuma wani ma’aikacin asibitin ya shaida wa wakilin Gidan Radiyon VOA Hausa cewa ya ga shigar motoci samfurin Hilux har guda biyar sun kai gawawwaki a cikin asaibitin a ranar Laraba.

Yayin da Jami’ar ta cika da alhini, shi ma kakakin ta, Danjuma Gambo yak i cewa komai, sai dai kawai ya ce yanzu magana ta na hannun jami’an tsaro.

Sojojin da aka rasa

Duk da cewa kakakin rundunar sojoji bai bayar da cikakken bayanin sojojin da aka rasa ba, PREMIUM TIMES ta samu sunayen su, sai dai ba za ta bayyana ba, har sai bayan an sanar da iyalan su tukunna.

Sun hada da Laftanar daya, Kofur biyu, Lanse Kofur daya da Karabiti biyar.

Share.

game da Author