PDP: Hankali ya kwanta tun bayan samin nasarar da muka yi a kotu – Makarfi

0

Shugaban jam’iyya PDP Ahmed Makarfi ya ba da shawara ga jam’iyyar da samar da wata doka a kundin tsarin mulkin jam’iyyar da zai sa shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar BOT ya zama shugaban jam’iyyar na rikon kwarya duk lokacin da aka sami matsalar shugabanci a jam’iyyar.

Makarfi ya ce zai mika wannan shawara tashi ga ya’yan jam’iyyar da ke yi wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar garanbawul.

Ya ce yin haka zai taimaka wajen hana wasu hayewa kan kujerar mulkin jam’iyyar ba tare da amincewar jam’iyyar ba.

Bayan haka makarfi yayi kira gay a’yan jam’iyyar da su hada kansu sannan su bude hannuwansu domin rungumar duk wanda yake da sha’awar shigowa jam’iyyar ko kuma dawo wa jam’iyyar.

“ Tun bayan samun nasara a Kotu da muka yi mutane sun kwantar da hankulansu domin suna ganin yanzu an samu mafita daga wahalar da ake fama dashi a kasar. Yanzu mutane suna ganin sun sami jam’iyyar da zasu jingina da shi fice wa daga wahalar da ake ciki.”

“ Dole mu hada kai dukkan mu ya’yan jam’iyyar domin samun nasara. Sannan mu jawo mutanen da suka fice daga jam’iyyar da hannu bibbiyu.”

Share.

game da Author