Likitoci a Faransa sun gano maganin cutar Hepatitis c

0

Wasu kwararrun likitoci a kasar Faransa sun gano wata sabuwan maganin kawar da cutar Hepatitis C mai suna ‘Direct-Acting Antivirals (DAAs)’.

Farfesa a asibitin Saint Antrine Karine Lacombe ta sanar da hakan a taron wayar da kan mutane akan cutar kanjamau da hukumar kula da gudanar da bincike IAS ta shirya a Paris ranar Litini.

Karine Lacombe ta ce hakan ya yiwu ne bayan gudanar da bincike don nemo maganin kawar da cutar da likitocin su kayi sannan da gwada ingancin maganin da suka yi a wasu kasashen Afrika ga mutanen da ke dauke da cutar.

Ta kara da cewa sun gwada ingancin maganin DAA akan mutanen 120 da suka kamu da cutar Hepatis C na tsawon makonni 24.

Ta ce binciken ya nuna musu cewa maganin ya warkar da kashi 89 bisa 100 na cutar a jikin mutanen.

Daga karshe darektan hukumar kula da gudanar da bincike kan cututtukar kanjamau da Hepatitis na kasar Faransa ANRS Framcois Dabis ya koka kan matsalar rashin isassun bayanai akan ingancin maganin musamman a kasashen dake fama da karancin maganin.

Share.

game da Author