Sanin kowa ne cewa sau da yawa gwamnati ta sha cewa ko an kashe shugaban Boko Haram Abubakar Shekau, ko kuma anji masa rauni a harin soji ko kuma,…
A duk lokacin da suka fito suka ce haka kwanaki kadan Shekau kuma yakan saki bidiyo ya na karyata sanarwan gwamnati da suka ce ko an kashe ko an ji masa ciwo.
A lokutta da dama saurin fadin hakan yakan tunzura kungiyar su fara kai farmaki ga mutane da sojoji babu kakkautawa.
Masu sharhi sun yi rubuce rubuce akan haka inda mafi yawa daga cikinsu suka nuna cewa fadin hali da shirin Sojin Najeriya na kara samar wa shi Shekau bayanai domin sake shiri ko canza dabara.
Tun bayan sanawar da rundunar Soji ta yi cewa ta ba shugaban rundunar (Operation Lafiya Dole) kwanaki 40 ya kamo Shekau aiyukansu ya sake sabon salo.
Ma’aikata da malaman jami’ar Maiduguri da sojojin da ba a san yawansu ba ne suka rasa rayukansu a wata harin kwantar bauna da Boko Haram ta kai musu. A rahotannin da ake ta samu daga gidajen yada labarai kusan dukkansu babu wanda ya tsira da ransa.
Ranar Juma’ar da ta gabata kuma wasu yan kunar bakin wake sun kai hari gari Dikwa. Inda aka rasa mutane 8 wasu kuma 15 suka jikkata.
A ganina saurin nuna samun nasara da rashin yin isasshen nazari kan yadda za a tunkari Boko Haram na daya daga cikin ababen da ke sa ana samun irin wadannan hare-hare musamman na dan kwanakinnan.
Idan da za’a ci gaba da nazari da samar da bayanan sirri ga sojojin da hakan kila zai ragu sanna a iya samun nasara akan abin da aka sa a gaba.
Ba sai rundunar sojin ko ma’aikatar tsaro ta yi shelar yadda zata tunkari Boko Haram a kafafen yada labarai ba. Fadin nasarorin ta yafi.
Wani abu kuma shine dole ne gwamnati ta inganta kula da take ba dakarun ta da ke fagen daga ta hanyar wadata su da makamai da kula.
Allah ya kawo karshen haka, Amin.
Discussion about this post