KADUNA-ABUJA: Za mu kara zafafa farautar barayin hanyar – Dambazau

0

Ministan aiyukkan cikin gida Abdulrahman Dambazau ya ce gwamnatin za ta kara tabbatar da ta inganta tsaro a hanyar Kaduna zuwa Abuja don ganin an kawar da fashi da satan mutanen da a ke yi kusan duk mako a hanyar.

Dambazau Ya fadi haka ne yake zantawa da manema labarai a Kaduna.

Ya ce hakkin gwamnatin ne ta kare dukiyoyi da rayukan mutane musamman yanzu da sace sace ke neman ya zama ruwan dare a wannan hanya.

Duk da cewa Sifeto janar din ‘yan sandar kasa Ibrahim Idris ya sanar da tura karin jami’an ‘yan sanda kusan su 600 a wannan titi har yanzu ana fama da wannan matsala na garkuwa da mutane.

Bayan haka Abdulrahman Dambazau a lokacin da ya ziyarci karamar hukumar Kajuru ya jinjina wa gwamnatin jihar Kaduna akan aiyukkan da take yi domin samar da zaman lafiya a jihar.

Ya shawarci mutanen yankin da su guji kai wa junan su hare-hare sannan ya tabbatar musu ta cewa gwamnati za ta hukunta duk wadanda ke neman tada zaune tsaye a yankin.

Bayan haka ya gana na gwamnan kaduna Nasir El-Rufai a gidan Sir Kashim Ibrahim, a Kaduna.

Share.

game da Author