An kafa kwamiti don samar da hanyoyin rage mutuwar mata masu ciki

0

Gwamnatin tarayya ta dauki mataki domin ganin cewa adadin yawan mutuwar mata masu ciki a kasar ya ragu. Ta yi haka ne ta hanyar kafa wata kwamiti wanda za ta tsaro hanyoyin kawar da matsalar.

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ne ya sanar da haka da ya ke kadamar da kwamitin a Abuja ranar Talata.

Ya ce kwamitin za ta gudanar da bincike a jihohi shida wanda suka fi samun yawa yawan irin wadannan matsaloli. Jihohin sun hada da jihar Zamfara,Kebbi,Sokoto,Yobe,Katsina da Jigawa.

Isaac Adewole ya ce an ba kwamitin tsawon watani uku su tsaro hanyoyinda za a bi don kawo karshen matsalar ganin yadda bincike ya nuna cewa Najeriya na daya daga cikin kasashe a duniya da fama da irin wannan matsala na rasa mata masu ciki.

Mayan bakin da suka halarci wannan taron sun hada da shugaban kungiya mai zaman kanta ‘Association for Reproductive and Family Health’ Oladapo Ladipo da sakatariyar ma’aikatan kiwon lafiya na tarayya Binta Adamu-Bello kuma duk sun ce kafa wannan kwamitin zai taimaka wajen gano yadda za a samar da hamyoyin da za abi don kubuta daga wannan matsala.

Shugaban kwamitin da aka kafa Adeniran Fawole ya tabattar da cewa za su gudanar da wannan aiki da aka basu cikin natsuwa da kwarewa.

Share.

game da Author