Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da rufe wasu asibitoci guda 18 da ke fadin jihar saboda rashin ciki sharuddan bude asibiti da basu dashi. Bayan haka kuma gwamnatin ta rufewasu shagunan siyar da magani guda 161.
Babban darekta a ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Bako Mohammed ne ya sanar da haka yau a garin Bauci. Ya ce ma’aikatarsa sun gudanar da bincike inda suka gano wasu da yawa daga cikin shagunan siyar da magani a jihar da na wasu kananan asibitoci a jihar basu da cikakken lasisin gudar da aiki.
Ya ce bayan binciken na su sun rufe wasu sannan wasu kuma sun ja musu kunne.
Asibitocin da gwamnati ta rufe guda 18 sun hada da : Nakowa Health Clinic, Bundon Rishi, Kowa Clinic, Lafiya Clinic, Mainasara Clinic, Jamare Clinic, New Edge, Na-Allah Na-Kowa, Makama Consultancy and Mahmud Health Clinic, duk a karamar hukumar Toro.
Sauran da aka rufe sun hada da, Taimako Clinic, Samson Clinic, Accelerated Dental, Al-Ihsan, Jibo a garin Bauchi, Zera laboratory da Dambam Medical laboratory duk a karamar hukumar Bauchi sannan da Salama Health Clinic dake karamar hukumar Bogoro.
Bayan haka ya yce gwamnatin za ta ci gaba da giudanar da irin wannan bincike a kananan hukumomi 19 dake jihar.
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar, Halima Mukaddas ta ta yi kira ga asibitocin jihar da shagunan sai da magani da su yi kokarin biyan kudaden harajinsu musamman yanzu da gwamnati ta sake gyara shi.
Discussion about this post