Gwamnatocin kasashen duniya za su tallafawa wa kasashe masu tasowa da kudade domin bunkasa shirin ba da tazarar iyali

0

Gwamnatoci da kungiyoyin ba da tallafi na duniya sun ware kudaden da ya kai dalla miliyan 2.5 domin samar da dabarun bada tazzarar iyali kyauta ga matan kasashe maso tasowa.

Sun sanar da bada wannan tallafi ne a taron da hukumar kidaya ta majalisan dinkin duniya UNFPA, gidauniyar Bill da Melinda Gates da kuma kasar Britaniya suka shirya domin wayar da kan mutane kan mahimmancindabarun bada tazaran iyali.

Jami’ar hukumar majalisar dinkin duniya Priti Ptel, mukaddashin shugabancin hukumar UNFPA Natalia Kanem da shugaban gidauniyar Bill da Melinda Gates Melinda Gates sun ce gwamnatin kasar Britaniya za ta ci gaba da bada tallafi kan dabarun bada tazaran iyali a duniya gaba daya daga nan har zuwa shekaran 2022.

Sun ce gwamnatin za ta maida hankalinta wajen samar da dabarun bada tazaran iyali ga matan kasashen da suka fi bukata musamman mazauna cikin sansanonin yan gudun hijra.

Bayan haka Natalia Kanem ta ce babbar matsalar da kan hana mata amfani da dabarun bada tazarar iyali shine yadda wasu kan kyamaci matan da ke amfani da shi.

Ministan kiwon lafiya na Najeriya Isaac Adewole ya ce Najeriya a shirye ta ke domin karfafa guiwar mata da ‘yan mata akan amfani da dabarun bada tazaran iyali domin guje wa daukan cikin da ba a bukata da kuma rage yadda ake zubar da ciki a kasar.

Share.

game da Author