An kama wani mai Anguwa da abokansa 6 sun yi wa wata ‘yar shekara 13 fyade a Kano

0

A ranar Talata ne rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani mai Anguwar kauyen Yargaya Alhaji Saje Sani dake karamar hukumar Dawakin Kudu da wasu abokansa shida da laifin aikata fyaden ga wata yarinya yar shekara 13.

Da ya ke tsokatawa manema labarai a Kano mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Magaji Majiya ya ce a yanzu haka likitoci sun tabbatar musu cewa yarinyar na dauke da cikin wata bakwai dalilin wannan lalata da akayi da ita.

Sannan kuma y ace sun kammala duk binciken da za suyi yanzu suna shirin maka su a kotu ne.

Bayan haka Majiya ya ce sun kashe wasu barayi da suka tare babbar titin Zariya zuwa Kano ranar Litini.

Ya ce sun yi arangama ne da barayin a lokacin da suke aikin fatirol akan wannan hanyan inda suka kashe biyu daga cikin su sannan sauran suka gudu da raunukar harsashi a jikinsu.

Majiya y ace sun kwato makamai da layun da ‘yan fashin suka bari sannan kuma ya yi kira ga mutane da ma’aikatan kiwon lafiya da su kai karan duk wanda suka gani da raunin harsashi a jikinsa zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.

Share.

game da Author