FYADE: Mata a garin Kano sun yi Zanga-zanga

0

A yau Talata ne wata kungiyar mata a jihar Kano ta gudanar da zanga-zangar lumana don nuna rashin jindadinta ga yadda fyade ga mata kanana ke neman ya zama ruwan dare a jihar.

Kungiyar da ta shirya wannan zanga-zanga ta hada tsoffin daliban makarantan sakandaren ‘Saint Louis’ dake Kano da wasu mata ma’aikata.

Sun ce sun shirya wannan zanga –zanga ne don gwamnati ta gaggauta daukan mataki kan matsalar.

Da suke zagayawa cikin gari, matan sun rike kwalaye dauke da rubuce-rubuce da yake nuna rashin jin dadinsu da abin da yake faruwa ga mata a jihar musamman a dan kwanakinnan.

Share.

game da Author