Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gode wa shugaban kasar Guinea Alpha Conde kan addu’oi na musamman da mutanen kasar suka yi masa wanda shi shugaban kasar ne ya shirya hakan.
Buhari ya kira Alpha Conde ne yau bayan wata wasika da ya rubuta masa a makon da ya gabata. Sannan ya kara mika godiyarsa ga Hadaddiyar kungiyar AU kan zaben sa don shugabantar wata kwamiti da ta kafa.
Buhari ya ce da zarar likitocinsa sun amince masa da ya komo gida zai dawo don ci gaba da aikin gyara kasa.