Babban Bankin Najeriya ya ce ba zai yi wa maniyyata sassaucin Dala ba

0

Babbban Bankin Najeriya, CBN, ya bayyana cewa ba zai yi wa maniyyata masu tafiya Saudiyya da Isra’ila rangwame ko sassaucin Dalar Amurka a kan naira 200 ba.

Bankin ya kuma musanta bayanin Sanata Adamu Aliero na ranar Alhamis a Majalisar Tarayya, inda ya furta cewa bankin kan sayar wa da ‘yan kasuwa dala har naira 200.

“Wannan furuci ba gaskiya ba ne, ba mu saida dalar Amurka daya a kan naira 200.” Inji kakakin yada labaran CBN, Isaac Okorofor.

“Bai yiwuwa mu saida dala a kan naira 200. Farashin dala daya a bankuna shi ne tsakanin naira 305 zuwa naira 315.” Okorofor ya furta wa wakilin Premium Times haka.

Shi ma shugaban hukumar inganta tattalin arzikin kasashen Afrika, Odilim Enwegbara, ya bayyana wa Premium Times cewa CBN ba za ta iya maida canji zuwa naira 200 ba.

Haka kuma da yawan wasu ‘yan Najeriya da su ka bayyana ra’ayoyin su, sun ce ba su goyi bayan a yi sasssaucin ba, saboda yawan ‘yan Najeriya sun sha zuwa Hajji, ko kuma Isra’ila ziyara.

Share.

game da Author