AMBALIYA: Mutane 23 sun rasa rayukansu a jihar Gombe

0

Akalla mutane 23 ne suka rasa rayukansu a ambaliyar da akayi a jihar Gombe inda gidaje 12 suka salwanta.

Mutane 6 sun rasu ne a garin Dadinkowa da ke Yamaltu-Deba sannan wasu 16 a garin Gombe.

Bayan haka gonaki 119 ne a garin Jauro Baba, Jauro Mai da Jauro Saini dake gundumar Kamo, karamar hukumar Kaltungo suka salwanta sannan kuma an yi hasarar abinci da taki sanadiyyar wannan ambaliya da ya ke ta aukuwa a sassan jihar.

Shugaban hukumar samar da agaji na jihar Mohammed Garba ne ya sanar da haka.

Share.

game da Author