Yadda wasu Sanatoci su ka karbi cin hanci kafin su amince da Kudirin Hukumar Tsaro ta Peace Corps

0

Kafin Sanatoci su amince da kudirin Hukumar Tsaro ta Peace Corps, sai da su ka karfbi cinnhanci da rashawar da su ka hada da ba su gurabun samar da aikin yi da kuma makudan kudade daga masu neman kafa hukumar. Hada dai Premium Times ta tabbatar.

Bayanai sun tabbatar da cewa wasu mambobin Majalisar Dattawan sun karbi gurabun samar da aikin yi guda bakwai kowanen su da kuma wasu nau’ukan kyautukan kafin su amince da kafa wannan sabuwar rundunar samar da zaman lafiya.

Bincike ya tabbatar da cewa wasu Sanatocin masu ruwa da tsakin shigar da dokar sun samu har gurabun aiki 500.
Wasu kuma sun karbi toshiyar baki na tsabar kudade masu yawa cikin su kuwa har ma da wadanda aka bai wa gurabun samar da ayyujan din.

Wannan harkallar dai ta zama abin tonon silili, har sai da ta kai wasu mambobin kwamitin su na fitowa kuru-kuru su na nuna wasu da yatsa cewa sun karbi cin hanci.

Amma kuma shugabannin Majalisar Dattawa sun shiga cikin maganar, inda suka sasanta Sanatocin masu yi wa juna kallon-hadarin-kaji, aka rufe maganar, inda aka tserar da Majalisar Dattawa daga shan kunya a fili. Haka wata majiya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES.

Sai dai kuma Hukumar Dakarun na Peace Corps ta musanta cewa ta bayar da toshiyar-baki ga sanatocin, a matsayin neman su amince da hukumar a karkashin dokar kasa, abin da su ka dauki shekaru goma su na gaganiyar neman tabbatar da haka.

“Kos au daya hukumar mu ba ta taba bayar da cin hanci ko toshiyar baki bag a Majalisar Dattawa.” Haka kakakin hukumar Milicent Umoru ya bayyana wa Premium Times.

“Gaskiyar magana wannan kudiri ya dade ana sa-toka-sa-katsi a kan sa kafin a amince da shi, ya zama doka a ‘yan kwanakin da su ka gabata.

Dukkan majalisu biyu dai sun amince da kudirin ya zama doka ne, “saboda sun ga mahimmancin tilasta tabbatar da wannan hukuma domin samar da aikin yi ga dimbin matasan Nijeriya. Haka ta kara jaddadawa.

Sai dai kuma har yau ba a sani ba har zuwa Asabar da ta gabata ko su ma mambobin Majalisar Tarayya sun karbi toshiyar-bakin kafin su sa wa dokar hannu ko a’a.

Majalisar Dattawa dai ta amince da wannan kudiri ya zama doka ne a ranar Talatar da ta gabata, duk da korafin da kwamitin majalisar dattawan kan ‘Yancin Dan Adam, Shari’a da Harkokin Kotu su ka yi cewa kudirin ba shi da wani amfani da jama’a.

Sanata David Umoru ne shugaban kwamitin da aka dora wa nauyin duba muhimmancin kafa hukumar ko rashin sa, kuma aka ce ya gabatar da binciken su a ranar Talata da ta gabata. Ya bayyana cewa:

“Wannan iko da ayyuka na hukumar dakarun tsaro din nan abin damuwa ne fa, kuma wannan kwamiti na mai neman a kara samun lokacin da za a sake bincikar sa dalla-dalla.”

Umoru ya kara cewa kokarin da masu neman a kafa wannan hukuma su ka rika yi, abu ne mai cike da alamar tambaya, domin kwata-kwata bai yi kama da hanyoyin da aka bi aka kafa irin sa a Amurka ba.”

“ Sannan kuma duk wannan hakilo da ake ta yi fa za a dauki ma’aikatan hukumar aiki ne na wa’adin shekara biyar kacal. Wadanda za su yi aikin don sa kai kuma shekara biyu kacal za su yi.”

Sai dai kuma duk da haka, sai Sanata Umoru ya roki majalisa ta amince da kudirin ya zama doka, yadda har Shugaban Kasa zai sa masa hannu.

Amma kuma shi Kwamandan Hukumar Dickson Akoh, y ace wannan hukumar za ta yi wa jama’a aiki da kuma amfani, fiye ma da yadda irin ta key i a Amurka.

Yayin da hukumomi da dama su ka muna rashin amincewa da kafa wannan hukuma, har yanzu Shuagaba Muhammadu Buhari da Shugaban Riko Yemi Osinbajo ba su ce za su sa wa kidirin hannu ya zama doka, ko ba za su sa masa hannu ba.

Duk kokarin jin ta bakin kakakin maganar Buhari, Malam Garba Shehu, Femi Adeshina da Laola Akande na Osinbajo ya ci tura. An yi kokarin kiran wayoyin su, amma ba su amsa ba.

Wata majiya a majalisa ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa an bai wa wasu ‘yan majalisar makudan kudi da kuma guraben aiki dubu daya.

Sai dai kuma Premium Times ba ta sami tabbaci ko David Umoru shi ma ya karbi toshiyar baki ko a’a ba.

Share.

game da Author