Andawo da ciyar da Daliban makarantar firamare a Kaduna

0

Gwamnatin Tarayya ta karbi ci gaba da ciyar da daliban makarantar Firamare a Kaduna daga ranar 25 ga watan Yuli.

Babban Darekta mai kula da shirin ciyar da daliban firamare a ma’aikatan Ilimi, John Gora ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ciyar da daliban firamare sai dai wannan karon za’ a ciyar da daliban aji 1-3 ne kawai.

John ya ce za a kashe sama da Biliyan 1 duk wata a wannan Shirin sannan za a ciyar da dalibai 800,000 a makarantun jihar.

“Za a kashe miliyan 56 duk rana, miliyan 280 duk wata sannan biliyan 1.1 duk wata.

“Yadda shirin yake yanzu, gwamnatin tarayya za ta ciyar da daliban Aji 1-3, sannan gwamnatin jihar ta ciyar da yan aji 4-6.”

Duk da cewa gwamnatin Tarayya bata gama biyan jihar Kaduna kudaden da ta kashe a wancan karon ba, ba za ta ci gaba ba sai ta kamala biyan ta. Amma yanzu ita za ta ciyar da yan Aji 1-3.

Share.

game da Author