A gyara dokar aikin ‘yan sanda saboda ta kunshi nuna wa mata bambanci –Sanata Remi Tinubu

0

An bayyyana bukatar kawo gyara ga dokokin da suka kafa aikin ‘yan sanda, saboda sun a tattare da nuna bambanci ga mata. Sanata Oluremi Tinubu ce ta bayyana haka yayin da ta ke gabatar da kudiri domin neman kawo gyara ga dokar.

Kudirin wanda ta ke son a gyara dokar aikin dan sanda ta 2014, Remi ta ce aikin dan sanda aiki ne mai matukar muhimmanci domin su ne ke kula da bin doka da oda da kuma tabbatar da zaman lafiya a cikin kasa.

Sanatar wadda ta fito daga Lagos, ta ce dokar daukar aikin dan sanda ta nuna bambanci ga mata. Yayin da aka amince a dauki namiji dan shekara 17, mata kuma sai daga shekara 19.

Sannan kuma ta nemi a gyara dokar aikin dan sanda ta sashe na 44 wadda ta ce duk wanda aka kama yay i wa aikin dan sanda sojan gona, to hukuncin sa tarar naira 200 ko kuma daurin shekara daya a gidan kurkuku.

A kan haka ne ta ce idan aka yi duba da idon basira, za a ga cewa hukuncin tarar naira 200 ko kusa bai kai karfin hukuncin mai laifin da ya yi sojan gonar aikin dan sanda ba.

Don haka ta ce, laifin sojan gona laifi ne babba wanda ya kamata a ce an tanadi hukunci mai tsauri ga wanda ya aikata shi.

Sanatocin dai sun goyi bayan wannan kudiri da ta gabatar, ciki kuwa har da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, wanda ya ce za su duba kuma su mika wa kwamitin kula da aikin dan sanda wanda shi kuma zai dawo masu da kudirin nan da makonni hudu.

Share.

game da Author