Sufeto Janar na rundunar ‘yan sandan kasar nan, ya bayyana cewa ana bukatar naira tiriliyan 1.13 a duk shekara domin ‘yan sandan Nijeriya su rika gudanar da ayyukan su yadda ya kamata su yi.
Ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata, a lokacin sauraren bayanai kan kudirin dokar da ta kafa Gidauniyar Farfado da Aikin ‘yan sanda ta 2004, a Abuja.
Sufeto Janar din ya kuma shaida wa kwamitin majalisar wakilai ta tarayya mai kula da kwamitin gyara aikin ‘yan sanda, cewa abin da ake kashewa kan ‘yan sanda ko kusa bai kai adadin da ya ce ake bukata ba.
Ya kara da yin bayanin cewa, wannan adadi da ya ce , bai ma hada da makudan kudaden da ake yin wasu manyan ayyuka da su ba, kamar sayen bindigogi da albarusai, motocin hidimar aikin tsaro, kananan kwale-kwale masu dauke da bindigogi, jirage masu saukar ungulu da sauran kayan da ake bukata na dole.
Idris har ila yau ya kara da cewa rundunar ‘yan sanda ta na bukatar akalla naira bilyan 26.9 a kowace shekara, a matsayin kudin kanikancin motocin rundunar da suka lalace da kuma kula da motocin kan su, da ya hada har da kudin zuba masu mai.
Ya kuma ce ana bukatar naira bilyan 200 a duk shekara domin a dasa kyamarori da kwamfutocin tattara bayanai a dukkanin ofisoshin ‘yan sanda da ke fadin kasar nan.