Za a dauki sabbin malaman makarantun Firamare da Sakandare a jihar Katsina

1

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da fara tantance mutane 3,000 da suke nemi aikin koyarwa a jihar.

Shugaban ma’aikatar SUBEB Lawal Buhari a jihar ya sanar da hakan inda ya ce kwamitin tantance ma’aikatan za ta fara ne da tanttance takardun gama makaranta wadanda suka nemi aikin.

Ya baiyana cewa wadanda suka sami nasara a jarabawar daukan malaman da jihar ta gudanar daga masarautar Daura da ya hada da Sandamu, Mai’adua, Baure da Zango sun kai su 722.

Buhari ya jinjinawa gwamnan jihar Katsina Aminu Masari kan kokari da yake na ganin ya bunkasa fannin ilimi a jihar ta hanyar gyara ajujuwan makarantu da kuma samar da ababen da makarantan ke bukata.

Daya daga cikin mambobin kwamitin tantancewar kuma kwamishinan matasa da wasani Abdullahi Abu ya ce za su kwatanta yin gaskiya da adalci yayin gudanar da aikin su.

A takaice dai jihar Katsina zata dauki malaman makaranta 1,900 wanda za su yi aiki a makarantu firamare da sakandare a jihar.

Share.

game da Author