Ba mu yarda da shirin muzguna mana da Majlisar Taraba ke shirin yi da sabuwar Dokar hana kiwo ba- Fulani Makiyaya

0

Makiyaya, mahauta da masu kasuwancin dabobi sun gudanar da zanga-zanga domin hana kafa dokar kiwata dabbobi a fili da majalisar dokokin jihar Taraba ke kokarin yi.

Sun yi wannan zanga–zangar ne da safiyar ranar Talata inda suka yi barazanar fara yajin aiki idan majalisar bata saurare su ta kafa dokar.

Masu zanga-zangar sun hau babbar titin Jalingo suna cewa kafa dokar zai takura makiyaya musamman aiyukkan kiwon da Fulani ke yi.

Sun kuma yi kira ga ‘yan majalisan da su janye wannan dokar da gwamnan jihar Dairus Ishaku ke kokarin kafawa domin zaman lafiya.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah na reshen Arewa maso gabacin Najeriya Umar Danburam ya ce “tun da farko ba a nemi a ji ra’ayoyin mu ba akan wannan doka sannan kafa dokar zai saba wa tsarin mulkin Najeriya”.

“Saboda haka idan ku ‘yan majalisa kun kafa wannan dokar za mu canza ta a kotun koli”.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Taraba Sahabi Tukur ya ce “Muna so mu shawarci ‘yan majalisan da muka zaba da su guje wa kafa dokar da zai hana zaman lafiya a jihar”

Kakakin majalisan wakilai Abel Diah a lokacin da ya karbi masu zanga-zangar ya soki wannan barazanar da suka yi domin a ra’ayinsa sun yi zanga-zangar ne ba tare da sani ba.

“Saboda hakan ina kira ga duk wanda ke da matsala da wannan dokar da ya halarci taron da aka shirya domin wayar da kan mutane kan wannan doka’’

Ya yin da Diah ke magana sai ‘yan zanga-zangar suka daga muryar da karfi su suna cewa “Karya Ne! Bama So, Bamu Yarda ba,” sannan shugabanin kungiyar na kokarin kwantar da hankalinsu.

Daga karshe dai yace majalisar za ta ci gaba da abin da ta sa a gaba.

Share.

game da Author