Mahukunta a kasar Tunisia sun daure wani mutum har na tsawon wata daya bayan kama shi da akayi yana shan lemu da zukar taba sigari a lokacin da kowa keyin Azumi.
Kungiyar Amnesty International ta yi tir da hakan da gwamnatin Tunisia din ta yi cewa yin hakan tauye hakkin sa ne.
Wannan mutum dai shine na biyar da aka kama a kasar suna cin abinci a bainar jama’a a wannan wata na Ramadan.
Dukkansu dai an yanke musu hukuncin zama a gidan yari na tsawon wata daya.
Ko da yake hakan na faruwa a wasu kasashen larabawa, a kasar Masar babu wata doka da gwamnatin ta yi da zai hukunta duk wanda ya aikata irin wannan laifi. Mahukunta na daukar wannan hukuci a hannunsu ne.
Kungiyar Amnesty International ta yi kira ga gwamnatocin kasashen da hakan ke faruwa da su dakatar da yin hakan sannan su kyale kowa ya aikata abinda yake so batare da an muzguna masa ba.