Wata mata mai ciki mazauniyar garin Falu dake karamar hukumar Guyuk ta rasa ranta sanadiyar duka da tasha wajen mutanen garin kan zargin maita da akayi mata.
Kwamishinan rundunar ‘Yan sandan Jihar Moses Jitoboh ne ya sanarwa manema labarai haka a garin Adamawa.
Moses ya ce wasu matasa ne suka far ma wannan mata inda sukayi ta dukan ta da sanduna sannan suka daddaure ta da igiya.
“ Matasan sun zarge ta da maita inda suka danganta rashin lafiya da mutuwar wasu mutane a kyauyen da ita.
“ Wadanda suka aikata hakan sun hada da Abraham Adamu, 18, Malachi Yilafane, 35, Thomas Aji, 54, Zakariya Chorum, 56 da wata Newana Ilihal ‘yar shekara 20.”