‘Yan matan Chibok sun gama karatu a Amurka

0

Wasu yan Matan Chibok da suka gudu bayan Boko Haram sun yi garkuwa dasu sun kammala karatunsu a wata makaranta dake Kasar Amurka.

Yan matan masu suna Debbie da Grace sun gudu ne bayan sun isa masaukinsu. Kafin Boko Haram su ankara sun bi dare cikin kungurmin dajin Sambisa inda suka dawo gidajensu.

Debbie da Grace na daga cikin ‘yan mata 57 da suka tsira a wancan lokacin. Na karshen su ita ce wata Halima Ali wanda ta gudu shekara biyu da suka wuce.

Wata kungiya ce mai zaman kanta ta dauki nauyin yaran.

Share.

game da Author