Bayan Muhammadu Buhari ya yi takarar shugaban kasa har sau uku, a 2003, 2007 da 2011 ya na faduwa zabe, ya yi nasara a karo na hudu a 2015. A wannan tattaunawa da UMAR ARDO ya yi da PREMIUM TIMES, ya bayyana dalilan da ya sa Jonathan ya fadi zaben 2015.
PTH: Gwamnatin Buhari ya cika shekara biyu. Idan za ka yi la’akari da nasarorin gwamnatin da kuma alkawurran da ta APC ta dauka, me za ka iya yin sharhi a kai?
ARDO: To ni dai ban san alkawurran da APC suka yi ba, amma dai bari mu duba wadannan kudirori uku, wato matsalar tsaro, cin hanci da kuma tattalin arziki. Ka san ni mutum ne mai kaushin sukar ra’ayi.
A fannin tsaro dai wannan gwamnatin ta dakile Boko Haram. Kasancewa na fito daga jihar Adamawa, zan iya tabbatar da haka. Duk da dai har yanzu akwai sauran ‘yan hare-hare da su ke kaiwa jifa-jifa. Amma fa akwai matsalar ‘yan sari-ka-noke a Neja Delta, masu garkuwa da mutane, fashi da makami, kashe-kashe, rikicin kabilu da sauran su.
To ka ga kenan a fannin tsaro, an dakile ta’addanci kawai zan ce, amma sauran matsalar tsaro da ta shafi al’umma, har yanzu dai kam ba mu rabu da su ba.
Akwai bukatar kara zage damtse domin a samu nasarori sosai. Ko a fannin yaki da cin hanci ai za ka ga abin duk bulkara ce ake ta yi. Ai daga batun harkallar Babachir kadai za ka iya gane cewa wannan gwamnatin ta daburce, ta rasa hanyar da ake bi a dakile cin hanci.
A fannin tattalin Arziki kuwa, kada mu manta har yanzu mu na cikin matsalar rudanin matsalar tattalin arziki.
Farashin canja naira ya wuce hankalin masu hankali. A halin da ake ciki yanzu, ba zan iya cewa wannan gwamnatin ta yi wata rawar gani ba.
PTH: Ka bugi kirji ka je kotu domin ka sa a hana Jonathan tsayawa takara. Domin a ganin ka, idan ya ci zabe a karo na biyu, a 2015, to zai shafe shekaru sama da takwas kenan a matsayin sa na shugaba, sabanin yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya amince. Shin ka na ganin faduwar zaben da Jonathan ya yi kamar wata sakayya ce aka yi maka?
Ardo: Kamar yadda ka ce na je kotu domin hana Jonathan tsayawa takara, tunda bai cancanci ya tsaba ba. Amma ai Kotun Komi sai ta ki yin la’akari da wannan batu. Amma a halin yanzu ina rubuta littafi inda na ke tattara bayanan darussan da na koya a kotu, dangane da wannan batun kai Jonathan kara da na yi a cikin 2014.
Littafin na kunshe baubawan-burmin hukunci da aka yanke dangane da kararraki goma da na kai Jonathan. Littafin zai fito cikin wannan shekarar.
PTH: Mutane da yawa sun yi magana a kan faduwar PDP zabe a 2015. Kwanan nan Jonathan ya dora laifin a kan Amurka. Kai a ganin ka me ya kawo faduwar zaben jam’iyya mai mulki a karo na farko a kasar nan?
Ardo: Na taba amsa wannan tambaya tun a cikin watan Yuli, 2015, a wata makala da na rubuta kuma aka buga. Yanzu kuma na karanta littafin Shegun Adeniyi, inda Jonathan ya yi wannan zargi. Sai dai a littafin akwai tasgaro sosai a ciki, kuma bai tabo muhimman wasu abubuwa ba.
Littafin bai yi maganar musabbabin kawancen jam’iyyu ba, sake tsayawar Buhari takara da kuma nasarar sa. To kuwa duk wani sharhin zaben 2015 in dai babu batun asalin karar da CPC ta kai kan kalubalantar zaben 2011 da abin da ya biyo baya, to littafin ba sahihi ba ne.
Ai kakuduba da kitimirmirar kotun daukaka karar zaben 2011 da kuma tayar da ikirarin da Buhari ya yi da farko cewa ba zai daulaka kara da sake tsayawa zabe ba, da kuma kawancen da ya haifar da APC, ai su ne tushen labarin zaben 2015. Zan iya tuna cewa ranar 16Ga Afrilu, CPC ta je kotu ta kalubalanci zaben 2011, kwanaki uku bayan Buhari ya ce shi ba zai je kotu ba. Sai kuma Buhari ya sake tsayawa takara a 2015., kenan Buhari ya warware ikirarin sa kenan.
Magana a nan ita ce, me ya faru Buhari ya tada alkawarin sa?Me ya sa CPC ta tafi kotu bayan Buhari ya ce ba zai je kotu ba? Ya batun kawancen da haifar da APC? Idan har ba a tattauna wadannan ba, to ban ga yadda za a ce littafi dangane da zaben 2015 zai zama sahihi ko ingantacce ba.
Kama daga littafin da Paden ya rubuta har na Adeniyi, babu inda su ka tattauna batun abinda ya faru bayan karar zaben 2011 da kuma kutunguitar cire Mai Shari’a Ayo Salami. Tunda kuwa duk babu wadannan, tilas a cikin littafin Paden da na Adeniy a ci karo da matsaloli da barababiya da soki-burutsu da shirme har ma da kazafi.
Bari ka ji, Jonathan ya fadi zaben 2015 tun ma daga ranar da ya cire Ayo Salami daga shugabancin kotun daukaka kara, a wata ranar Lahadi. Daga nan kawance ya yanke tsakanin PDP da ACN. Daga nan aka kulla tsakanin ACN da CPC, har aka kafa APC.
Ai ka ga ba don CPC ta je kotu ba, da ba a tsige Salami ba. Da ba a tsige Salami ba, da ACN ba ta rungumi CPC din Buhari ba. Da ACN ba ta rungumi CPC ba, da ba su yi kawance ba. Da ba a yi kawance ba, da ba a kayar da Jonathan ba.
PTH: Kenan ka na ganin dabarar siyasa ce ta sa Buhari ya tsaya takara a karo na hudu tunda ya ga alamun nasara bayan ya ce ba zai sake tsayawa takara ba?
Ardo: Zan iya cewa kusan ya ga alamomin nasara din. Bayan na baje masa wannan asarkalar a faifai, na tashi na fita, sai ya kira ni a waya ya ce min na amince da shawarar ka. Ka je ka aiwatar da su. Bayan wannan duk wani abin da ya biyo baya, ya zama tarihi, ka ji sila.
PTH: To ai kai ka zame wa PDP kara-da-kiyashi kenan. Ya aka yi ka na dan PDP amma ka kulla mata tarnaki da dabaibaiyin da ya haifar da faduwa zabe? Abin kamar akwai dalilin kabilanci ko addinanci ko?
Ba haka ne. Magana ce ta Nijeriya. Ai a 2007 an shirya ba Peter Odili takara, wanda dan yankin su Jonathan ne. Ma’ana idan Obasanjo na Kudu maso Yamma ya gama shekara takwas, sai dan Kudu maso Kudu ya yi wata takwas kenan. Tunda yanki ne mai zumuncin siyasa da Arewa.
PTH: Wasu na ganin kasa sasantawa da Jonathan ya yi da ACN da kuma batun Tambuwal a matsayin kakakin majalisa ya haifar da faduwa zaben Jonathan. Haka ne?
Ardo: Hakan ne dai tushe, amma tsige Ayo Salami ne ginshikin faduwar Jonathan.
PTH: A karshe, jam’ iyyar ka PDP fa ta kamo hanyar tarwatsewa kamar yadda wasu ke fadi. Ka yarda?
Ardo: PDP ba za ta tarwatse ba, ba za mu bari ta tarwatae ba. Bari mu jira sakamakon hukuncin Kotun Koli tukunna. Daurin auren ‘yar Babangida ya isa ka lura cewa har yau PDP na nan da karfin ta. Wannan kuwa zai iya nuna wa mutane irin kokawar da za a yi a 2019.