Hanyoyi 9 da zaka bi domin kaucewa kamuwa da cutar murar tsuntsaye

0

Dalilin bullowar cutar murar tsuntasye wani likita ya bada hanyoyi tara da za a iya bi domin kauce wa kamuwa da cutar.

Ga hanyoyin:

1 – A guje wa shafan tsuntsayen gida ko na daji da ke kamar basu da lafiya.

2 – A dafa naman kaji sosai har sai sun dahu sosai.

3 – Ka wanke hannayenka sosai da man kashe cuta na hannu bayan an taba wadannan tsuntsaye.

4 – Ka nisanta kanka da ga zuwa wuraren da ake kiwata tsuntsaye ko kasuwarsu.

5 – Ka nemi maganin rigakafin mura. Hakan zai rage kamuwa da cutar.

6 – Ka gujewa amfani da danyen kwai.

7 – Ka wanke cukula da kayan cin abincinka sosai musamman idan an yi amfani da su a irin wadannan wurare.

8 – Ka nisanta da duk wani wanda ya kamu da mura.

9 – Ka hanzar ta zuwa asibiti idan baka jin dadi.

Share.

game da Author