Za mu bi duk hanyar da zamu bi mu kwato dukiyar mutanen Jihar Katsina daga hannun Shema – Masari

1

Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya ce gwamnatin da ta gabata a jhar, wato gwamnatin Ibrahim Shema ta barnata kudaden Jihar da ya kai sama da Biliyan 50 a tsawon shekaru 8 da yayi yana gwamnan Jihar.

Masari ya fadi haka ne da yake karban bayanai akan sakamakon binken da kwamitin da gwamnatin Jihar takafa domin binciken ayyukan gwamnatin da ya gabata.

Gwamnan ya ce gwamnati ba za ta saka Ido ta bari wasu ‘yan kalilan su kwashe kudin jama’a ba  sannan ayi shiru.

Ya ce gwamnatin sa za ta yi kuma ta bi duk hanyar da zata bi domin ganin an kwato wadannan kudade a hannun jami’an gwamnatin baya da kuma wadanda shi kansa gwamnan ya waske da su.

Share.

game da Author