Wata mata mai suna Kudirat Sodiq ta sanar da wata kuto a jihar Legas cewa mijinta Wahabi na cizon ta duk lokacin da suka rincabe da fada a gida.
Kudirat tace yanzu duk jikinta tabon cizo.
Kudirat ta shigar da kara gaban kuto tana neman kotu tayi mata hannun riga da mijinta da suke shekara na 23 kenen da aure.
“ Akwai lokacin da mijina ya zo shagona dauke da kwalban giya in da ya fasa ya nemi kashe ni da shi. Allah ne ya cece ni ranar domin da kyar na sha.
“ Bayan haka kuma ya nemi da ya siyar da gidan da na gina amma hakan bai yiwu ba har yanzu.
Kotu to daga ci gaba da sauraron karan zuwa 15 ga watan Yuli.