Wani limami mai suna Aminulahi Seriki ya yi kira ga musulman Najeriya da su yi amfani da wannan dama na watan Ramadan domin yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a Allah ya bashi dawwamammiyyar lafiya.
Ya fadi hakan ne a lokacin da yake yin jawabi a taron da shugaban jam’iyyar PDP na jihar Legas Moshood Salvador ya shirya mai taken ‘’mahimmancin addu’a”.
Ya kuma gargadi al’ummar musulmai da a rage kallon tallabijin musamman a wanna lokaci na watan Ramadan.
“Bai kamata lokacin da mutum ke ibada ya dunga yi yana kallon tallabijin ko kuma kallon wasu abubuwan dake faruwa kusa da shi marasa anfani wanda hakan ke hana addu’o’i karban Addu’o’i”.
Limamin ya jinjinawa Moshood Salvador saboda shirya wannan taron da yake yi wanda hakan zai taimaka wajen karfafa musulmai.