Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta zuba zaratan ‘yan sanda 600 a kan titin Abuja zuwa Kaduna. Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, DIG Habila Joshak ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke kaddamar da rundunar ‘yan sandan na musamman, a kauyen Rijana, kan titin Kaduna zuwa Abuja, a cikin jihar Kaduna.
Joshak ya bayyana cewa ‘yan sanda 500 ne aka baza, saura 100 kuma jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma ne daga sashen leken asiri na fannin tsaron rundunar ‘yan sanda.
Sufeto Janar na ‘yan sanda Ibrahim Idris ne ya bayar da umarnin baza jami’an tsaron domin kara tabbatar da kare rayukan matafiya a kan titin Abuja zuwa Kaduna.
Ya ce nauyin jami’an tsaro ne kare rayuka, dukiyoyi da lafiyar jama’a, shi ya sa aka tsamo wadannan zaratan ‘yan sanda daga cikin zaratan da ke yaki da kakkabe Boko Haram da sauran su.
Daga nan sai Mataimakin Sufeton ya yi horo ga jami’an tsaron da su yi aikin su da gaskiya da kuma kishi, wajen kare rayukan jam’a da kuam tabbatar da tsaro a kan titin Abuja zuwa Kaduna da sauran wuraren da ke kewaye da hanyar.
Ya kuma ce za su yi aiki kafada-da-kafada da sauran jami’an tsaron da ba ‘yan sanda ba, wajen ganin an kakkabe matsalar sata da garkuwa da matafiya da ya zama ruwan-dare a kan titin.
Sai dai kuma idan ba a manta ba, cikin Agusta, 2016, an taba kaddamar da irin wannan rundunar jami’an ‘yan sanda, a Katari, kan titin Abuja zuwa Kano, har su 600, amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Wannan titi dai ya na fama da masu garkuwa da matafiya, masu cin Karen su ba babbaka, tun su na yi da tsakar dare, yanzu ma sun dawo su na tare hanya da rana tsaka.
Cikin makon da ya gabata, sun tare hanya da rana tsaka, inda rahotanni suka nuna cewa sun arce da matafiya har 20.