Asusun tallafawa wadanda fada wani hadari ‘Victims Support Fund’ (VSF) ta tallafa wa wasu asibitoci biyu a Maiduguri da gudunmuwar Naira miliyan 20 domin agaza wa mutanen da suka sami raunuka daga hare-haren da Boko Haram ta kai gain Maiduguri.
Asibitocin da suka sami wannan tallafi sun hada da Asibitin Koyarwa na jami’ar Maiduguri Da asibitin kwararru dake Maiduguri.
Shugaban gidauniyar Sunday Ochoche ne ya sanar da hakan a wata ziyara da ya kai asibitocin domin duba mutanen da ke kwance a asibitocin sanadiyyar hare-haren da Boko Haram ta kai garin na Maiduguri.
A shekarar 2015 gidauniyar ta raba Naira miliyan 20 ga wasu asibitocin domin kula da irin wadannan mutane.
Ochoche ya ce a takaice dai asibitin koyar wan a jami’ar Maiduguri (UMTH) ta sami Naira miliyan 30 sannan Asibitin kwararraru na (Borno State Specialist Hospital) ta sami Naira miliyan 20 ita ma.
Shugaban asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri Abdurahaman Tahir ya godewa gidauniyar VSF da irin wannan gudunmuwar da take ba asibitin musamman a wannan lokaci da asibitin ke bukatar haka domin taimakawa wadanda suka fada tsautsayin hare-haren Boko Haram.