Kotu ta yi watsi da karar Saraki

0

A yau Laraba ne kotun kula da ma’aikata, CCT, a Abuja ta kori karar da aka shigar gabanta wanda ake tuhumar Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki da laifuka har 13, ciki har da yin karya wajen rage yawan kadarorin sa a lokacin da ya bayyana yawan dukiya da kadarorin da ya mallaka a lokacin ya na gwamnan jihar Kwara.

Jami’in gabatar da kara M.S Hassan ne ya rubuta tuhumomin da ake yi wa Saraki, inda aka yi ta tabka shari’a har tsawon shekaru biyu. Idan ba a manta ba, cikin watan Mayu, 2017, an kara yawan caje-cajen da ake tuhumar Saraki zuwa 17.

Tun cikin watan Satumba, 2017 ne aka fara maka Saraki kotu.

Wasu tuhume-tuhume da ake yi wa Saraki, sun hada da mallakar dukiyar da ta zarce albashin sa da kuma bude asusun ajiyar kudade a kasashen waje.

Tun lokacin da aka maka shi kotu, Saraki ya yi ta cewa ana yin wannan shari’a ne don a bata masa suna ne.

Da yake karanta bayanin korar karar. Mai shari’a Umar, wanda tun farko Saraki ya ce bai yarda ya yi masa shari’a ba, ya bayyana cewa mai gabatar ga kara ya kasa gabatar da kwakkwaran hujjojin da za su tabbatar wa kotu cewa Saraki ya aikata zargin da ake yi masa.

Share.

game da Author