A Kula da yadda ‘yan gudun Hijra ke shigowa Najeriya daga Kasar Kamaru – Hukumar UNHCR

0

Jami’in hukumar kula da al’amuran ‘yan gudun hijra na majalisar dinkin duniya Filippo Grandi ya ce yadda ‘yan gudun hijra ke dawowa Najeriya daga kasar Kamaru zai iya tado wata sabuwar rashin kwanciyar hankali a yankin arewa maso gabas idan ba ayi maza maza an dubi abin ba.

Hukumar UNHCR a watan Mayu ta gargadi gwamnatin Najeriya akan hakan wanda a lokacin da ‘yan gudun hijira 12,000 suka dawo Najeriya ta bodar garin Bankin dake jihar Borno sannan ko a lokacin akwai ‘yan gudun hijira 45,000 dake zaune a garin.

Garin Banki gari ne da ke mutane da dama amma ya zama kango saboda aiyukkan Boko Haram wanda bayan hakan ne sojojin Najeriya suka kwato garin a watan Satumbar 2015.

Grandi ya ce a yanzu haka wasu ‘yan gudun hijira 889 wanda mafi yawansu yara ne sun shigo Najeriya ta bodar garin Banki a ranar 17 gawatan Yuni daga kasar Kamaru.

‘’A ra’ayina kamata ya yi a dakatar da dawowa da ‘yan gudun hijira musamman a wannan lokacin’’.

Grandi ya ce matsalar da suke fama da shi a garin shine yawan cunkoso na ‘yan gudun hijira wanda hakan ya sa sukan sami karancin kayayyaki na agaji.

Share.

game da Author