Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya ce gwamnati za ta karo sabbin taragon jirgin kasa guda hudu domin samun sauki wajen daukan matafiya daga Abuja zuwa Kaduna.
Amaechi ya fadi haka ne a wajen kaddamar da sabuwar tashan sauke kaya da aka bude a bude a Kaduna.
“Gwamnati na kokarin ganin cewa ta wadatar da isassun tarago da zasu dinga dibar mutane daga Abuja zuwa Kaduna a duk lokaci.
Ministan ya dada tabbatar wa mutane da kokarin gwamnati na kammala duk ayyukan titunan jirgin da ke gudana a kasa.
Ya ce gwamnati za ta karo wasu jiragen kasa da zaran ta kammala ayyukan titunan jirgin sannan za’a shigo da manyan tarago-tarago na kasaita ‘Business class’ wanda za su ding jigila daga jihohin Legas, Kano,Port Harcourt da Maiduguri’’.

03385/20/6/2017/Albert Otu/BJO/NAN